ABNA24 : Wani jami’in ‘yan sandan garin Waqar Azim ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa fashewar ta faru ne a yau din nan Talata a Jami’a Zubairia Madrassa da ke garin na Peshawar a lokacin da wani mutum ya shiga makarantar da wata jaka, ya ajiye ta fice inda nan ba da jimawa ba fashewar ta faru.
Shugaban ‘yan sandan garin Muhammad Ali Khan ya tabbatar da cewa mutane 7 ne suka mutu kana wasu da dama kuma suka sami raunuka.
Ya ce dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin wanda ya ce ana zargin bama-baman da aka makare su a cikin jakar da mutumin ya zo ya ajiye sun kai kilogram biyar zuwa shida na abin fashewar.
342/